Posts

Yadda muke rayuwa manne da juna shekara 22, in ji tagwayen da aka haifa manne da juna

Image
Carmen da Lupita tagwaye mata ne da aka haife su manne da juna shekaru 22 da suka shuɗe. Tagwayen sun bayyana yadda suke gudanar da rayuwarsu mai cike da al'ajabi  DAILY MAIL ya rawaito 'yan matan na cewa, saboda yanayin halittarsu hakan ya sa ya zama al'amari mai hatsarin gaske idan aka ce za yi musu aiki don a raba su. "Idan aka yi mana aiki don a raba mu, tilas ɗayanmu ta mutu, ko duka mu biyun mu mutu, ko kuma mu ƙarasa rayuwarmu a sashen ICU,” in ji Lupita. Game da mu'amalar soyayya kuwa, Lupita ta kasance ba ta jin sha'awa da makamancin haka balle ta ji tana buƙatar wani da zai riƙa ɗebe mata kewa, shi ya sa ma ba ta da saurayi. Amma ita Carmen tana da saurayi mai suna Daniel wanda suka haɗu ta wata manhajar da ke haɗa masoya a Oktoban 2020. Carmen ta ce, “Tun farko na san cewa Daniel mutum ne na daban, saboda farkon haɗuwarmu bai damu ya tambayi yaya yanayin hallitata ba. "Shekara biyu da rabi kenan muna tare, kuma mun tattau...

HOTUNA: Ɗaliban sashen nazarin kiɗe-kiɗe da raye-raye na Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, Jihar Anambara

Image
HOTUNA: Facebook / Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu / Jaridar Punch

An tsinci gawar ɗalibin jami'a a kan ruwa a Bayelsa

Image
A gano gawar wani matashi mai suna Bright Akhere, ɗan shekara 21, a cikin wata kwatarniyar wanka (swimming pool) a ranar Talata a wani otel da ke Otuoke, cikin Ƙaramar Hukumar Ogbia, Jihar Bayelsa. Jridar LEADERSHIP ta ce matashin ɗalibin aji biyu ne a Jami'ar Tarayya da ke Otuoke. Duk da dai babu cikakken bayani kan mutuwar matashin, sai dai bayanai sun ce, marigayin wanda ɗan asalin Jihar Delta ne, shi kaɗai ya tafi wanka a kwatarniyar a ranar Litinin. Daga nan kuma ba a sake jin ɗuriyarsa ba har zuwa lokacin da aka gano gawarsa a kan ruwa ranar Talata da misalin ƙarfe 7 na dare.

An fara kwashe 'yan Nijeriya da suka maƙale a Sudan zuwa Masar

Image
Hukumar kula da 'yan Nijeriya mazauna ƙetare, NiDCOM, ta ce an fara jigilar 'yan ƙasar da suka maƙale a Sudan zuwa Alƙahira, babban birnin Masar. Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Twitter ranar Laraba. Ana jigilar waɗanda lamarin ya shafa ne ta hanyar amfani da dogayen motocin da Nijeriya ta tanadar.

Sama da mutum 200 sun ɓace a dajin Shakahola

Image
Rahotanni daga ƙasar Kenya na nuni da cewa, adadin mutanen da suka ɓace a cikin dajin Shakahola ya ƙaru zuwa 212. Majiyarmu ta ce a halin da ake ciki, wajen ajiyar gawarwaki da ke yankin Malindi ya cika bayan da aka kai wasu gawarwakin mutum 78 da aka gano. Dajin Shakahola wuri ne da ke ƙarƙashin wata ƙungiyar asiri wadda Paul Mackenzie Nthenge ke jagoranta. Da alama dai Shakahola daji ne da ya yi ƙaurin suna a harkokin tsafi.

Sarakuna masu daraja ta ɗaya a Jihar Nasarawa

Image
Jihar Nasarawa da ke Arewa ta tsakiyar Nijeriya, na sarakunan gargajiya masu daraja ta ɗaya da duka haɗa da: 1. Abaga Toni  2. Sarkin Nasarawa 3. Andoma of Doma  4. Esu Karu 5. Aren Eggon 6. Gomo Babye 7. Chun Mada   8. Gom Mama 9. Sarkin Awe  10. Odyong Nyankpa 11. Sarkin Azara  12. Ohimege Opanda 13. Sarkin Lafia 14. Oriye Rindre 15. Sarkin Karshi   16. Osana of Keana 17. Sarkin Keffi  18. Sarkin Loko 19. Osu Ajiri  20. Osuko of Obi 21. Sangarin Kwandere 22. Zhe Migili  23. Sangarin Shabu 24. Osakio of Assakio 25. Sangarin Deddere 26. Ohinoyi Ogye 27. Sarkin Gurku 28. Osu Agwada

Kisan Jos: Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Jos-Abuja

Image
Rahotanni daga yankin Farin Lamba cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, sun ce jama'ar yankin sun yi dandazo a kan hanyar Jos zuwa Abuja ɗauke da gawarwakin waɗanda 'yan bindiga suka kashe a wajen wani mahaƙar ma'adinai a yankin. A ranar Talata da daddare 'yan bindiga suka kai hari yankin inda suka kashe mutanen da ba bayyana adadinsu ba. A ranar Laraba aka ga wasu mazauna Farin Lamba da wasu daga ɓangaren Ƙaramar Hukumar Riyom suka mamaye babbar hanyar da ke yankin ɗauke da gawarwakin wasu da kisan ya shafa.