An tsinci gawar ɗalibin jami'a a kan ruwa a Bayelsa
A gano gawar wani matashi mai suna Bright Akhere, ɗan shekara 21, a cikin wata kwatarniyar wanka (swimming pool) a ranar Talata a wani otel da ke Otuoke, cikin Ƙaramar Hukumar Ogbia, Jihar Bayelsa.
Jridar LEADERSHIP ta ce matashin ɗalibin aji biyu ne a Jami'ar Tarayya da ke Otuoke.
Duk da dai babu cikakken bayani kan mutuwar matashin, sai dai bayanai sun ce, marigayin wanda ɗan asalin Jihar Delta ne, shi kaɗai ya tafi wanka a kwatarniyar a ranar Litinin.
Daga nan kuma ba a sake jin ɗuriyarsa ba har zuwa lokacin da aka gano gawarsa a kan ruwa ranar Talata da misalin ƙarfe 7 na dare.
Comments
Post a Comment