Yadda muke rayuwa manne da juna shekara 22, in ji tagwayen da aka haifa manne da juna
Carmen da Lupita tagwaye mata ne da aka haife su manne da juna shekaru 22 da suka shuɗe.
Tagwayen sun bayyana yadda suke gudanar da rayuwarsu mai cike da al'ajabi
DAILY MAIL ya rawaito 'yan matan na cewa, saboda yanayin halittarsu hakan ya sa ya zama al'amari mai hatsarin gaske idan aka ce za yi musu aiki don a raba su.
"Idan aka yi mana aiki don a raba mu, tilas ɗayanmu ta mutu, ko duka mu biyun mu mutu, ko kuma mu ƙarasa rayuwarmu a sashen ICU,” in ji Lupita.
Game da mu'amalar soyayya kuwa, Lupita ta kasance ba ta jin sha'awa da makamancin haka balle ta ji tana buƙatar wani da zai riƙa ɗebe mata kewa, shi ya sa ma ba ta da saurayi.
Amma ita Carmen tana da saurayi mai suna Daniel wanda suka haɗu ta wata manhajar da ke haɗa masoya a Oktoban 2020.
Carmen ta ce, “Tun farko na san cewa Daniel mutum ne na daban, saboda farkon haɗuwarmu bai damu ya tambayi yaya yanayin hallitata ba.
"Shekara biyu da rabi kenan muna tare, kuma mun tattauna yi mana baiko, amma mun fi so mu kasance tare tukuna zuwa wani lokaci.”
Carmen ta ƙara da cewa, takan yi ƙoƙarin ganin sun yi wa 'yar uwarta Lupita sassauci duk lokacin da suka fita shan iskar soyayya tare da sauranyinta Daniel, wadda takan fita ba don ta so ba sai don a kan dole tun da suna manne da juna.
Don haka ta ce takan bai wa Lupita damar ta zaɓa musu kayan da ya dace su saka, inda za su ci abinci da sauransu, don ita ma ta ji daɗi.
Comments
Post a Comment