Sama da mutum 200 sun ɓace a dajin Shakahola

Rahotanni daga ƙasar Kenya na nuni da cewa, adadin mutanen da suka ɓace a cikin dajin Shakahola ya ƙaru zuwa 212.

Majiyarmu ta ce a halin da ake ciki, wajen ajiyar gawarwaki da ke yankin Malindi ya cika bayan da aka kai wasu gawarwakin mutum 78 da aka gano.

Dajin Shakahola wuri ne da ke ƙarƙashin wata ƙungiyar asiri wadda Paul Mackenzie Nthenge ke jagoranta.

Da alama dai Shakahola daji ne da ya yi ƙaurin suna a harkokin tsafi.

Comments

Popular posts from this blog

Kisan Jos: Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Jos-Abuja

Sarakuna masu daraja ta ɗaya a Jihar Nasarawa

Yadda muke rayuwa manne da juna shekara 22, in ji tagwayen da aka haifa manne da juna