Kisan Jos: Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Jos-Abuja

Rahotanni daga yankin Farin Lamba cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, sun ce jama'ar yankin sun yi dandazo a kan hanyar Jos zuwa Abuja ɗauke da gawarwakin waɗanda 'yan bindiga suka kashe a wajen wani mahaƙar ma'adinai a yankin.

A ranar Talata da daddare 'yan bindiga suka kai hari yankin inda suka kashe mutanen da ba bayyana adadinsu ba.

A ranar Laraba aka ga wasu mazauna Farin Lamba da wasu daga ɓangaren Ƙaramar Hukumar Riyom suka mamaye babbar hanyar da ke yankin ɗauke da gawarwakin wasu da kisan ya shafa.




Comments

Popular posts from this blog

Sarakuna masu daraja ta ɗaya a Jihar Nasarawa

Yadda muke rayuwa manne da juna shekara 22, in ji tagwayen da aka haifa manne da juna