An fara kwashe 'yan Nijeriya da suka maƙale a Sudan zuwa Masar
Hukumar kula da 'yan Nijeriya mazauna ƙetare, NiDCOM, ta ce an fara jigilar 'yan ƙasar da suka maƙale a Sudan zuwa Alƙahira, babban birnin Masar.
Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Twitter ranar Laraba.
Ana jigilar waɗanda lamarin ya shafa ne ta hanyar amfani da dogayen motocin da Nijeriya ta tanadar.
Comments
Post a Comment